Rashin kudi na cikas ga taimako a Syria- Save the Children

Kungiyar ba da agaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa, rashin kudi na kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi, na taimakon 'yan kasar Syria a yayin da sanyin hunturu ke karatowa.

Ta ce babu isassun tufafi da barguna da guraren da za su fake.

Kungiyar tace nan da 'yan makwanni dusar kankara da tsananin sanyin da za a yi, zai sanya 'yan gudun hijirar shiga wani mawuyacin hali.

Wasu kudade na musamman da aka ware don taimakon 'yan gudun hijirar sun samu nakasu da kimanin dala miliyan dari biyu.

A ranar litinin Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da cewa za ta janye ma'aikatan ta da ba su da muhimmanci a Syria, saboda dagulewar rikicin.

Karin bayani