Annan ya yi gargadi kan 'yan takara a Kenya

Image caption Kofi Annan, Tshohon Sakataren MDD

Tsohon babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan ya yi gargadi game da hadurran dake tattare da zaben 'yan takarar Shugaban kasa wadanda ke fuskantar tuhuma a Kotun hukunta manyan laifukka ta duniya.

Lokacin da yake magana da BBC a Nairobi, Mr. Annan ya ce zaben Uhuru Kenyatta ko William Ruto a zaben da za a gudanar a badi, zai rikita huddar dangantakar Kenya da sauran kasashen duniya.

Ana zargin dukkan mutanen biyu ne da hannu a miyagun laifuka na cin zarafin 'yan adam da aka aikata a rikicin da ya biyo bayan zabukan da aka yi a kasar shekaru biyar da suka gabata.

Mr Annan yace, "muna rayuwa ne yanzu da kasashe suka dogara da juna.

Inji Annan ya ce Kamata ya yi ace Shugaban wata kasa yana iya zuwa wata kasa, ya yi mu'amalla da Shugabannin ta."

Karin bayani