Gwamnatin Mali za ta tattauna da 'Yan tawaye

Image caption Masu kishin Islama a Mali

Gwamnatin kasar Mali ta amince za ta shiga tattaunawa da 'yan tawayen Abzinawa da na 'yan kishin Islama a wani kokari na sake hada kan kasar.

Bayan sun gana da jami'an gwamnati, kungiyoyin dake gaba da juna sun yi alkawarin mutunta 'yancin yankunan kasa na Mali, tare kuma da yin watsi da ayyukan ta'addanci.

Abzinawan da 'yan kishin Islama sun kwaci sassa masu yawa na arewacin Mali bayan wani juyin mulki da aka yi cikin watan Maris.

Shawarwarin da ake shirin gudanarwa ba za su hada da sauran wasu kungiyoyi biyu ba, masu fafutuka dake dauke da makamai wadanda gwamnati ta ce, sun kunshi mayaka ne 'yan kasar waje.

A kwana kwanan nan gwamnatocin yankin suka amince da wani shiri na tura sojoji sama da dubu uku zuwa arewacin kasar Mali, da za rar sun samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya.

Karin bayani