NATO za ta girke makaman kariya a Turkiyya

Image caption Shugaban kungiyar kawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta amince da bukatar kasar Turkiyya, na girke ma ta makaman kariya daga makamai masu linzami.

Turkiyyar ta nemi hakan ne domin tunkarar duk wata barazana daga tsallaken kan iyakarta da Syria.

Wasu karin makaman igwa da ake harbawa a rikicin kasar ta Syria, sun fada cikin kasar ta Turkiyya ranar Talata.

Ministocin harkokin waje na kasashen NATO dake taro a Brussels sun bayyana matukar damuwa, kan rahotannin cewa akwai yuwuwar Syria ta yi amfani da makamai masu guba a fadan da take yi da 'yan tawaye.

Shugaban kungiyar kawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce, idan Syria ta kuskura ta yi amfani da makamai masu guba, to kuwa kasashen duniya ba za su yi wata-wata ba, za su dauki mataki a kanta.

Gwamnatin Syriar dai ta tsaya kai da fata cewa, ba za ta taba amfani da makamai masu guba ba a kan al'ummar ta.

Karin bayani