'Najeriya ce kasa ta 35 a cin hanci a duniya'

Rahoton hukumar Transparency kan rashawa
Image caption Rahoton hukumar Transparency kan rashawa

Najeriya ce kasa ta 35 mafi fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya, a cewar rahoton da hukumar transparency international ta fitar.

A jerin kasashen da rahoton na bana ya fitar, kasashen Denmark da Fin Land da kuma New Zealand ne ke saman tebur, abin da ke nuna cewa su ne ke da mafi karancin matsalar cin hanci da rashawa a cikin kasashe 176 da hukumar ta transparency international ta yi bincike a kansu.

Yayin da kasashen Somalia da Afghanistan da kuma Koriya ta kudu ke kasan teburin.

Najeriya ta kasance kasa ta 139 a cikin kasashen baki daya, abin da ya sa ta zamo kasa ta 35 mafi fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya.

Kodayake a bara kasar ta kasance ta 37 a irin wannan rahoton da aka fitar a shekarar 2011, sai dai kuma yawan kasashen da hukumar ta yi nazari a kai a bara sun kai 183.

Yayin da Kasashen Nijar da Togo da Mali da kuma Benin suke saman Najeriya a jerin kasashen da hukumar ta yi binciken a kansu.

Ra'ayin masana

Wasu masana a Najeriyar kamar Dr. Usaini Abdu, shugaban kungiyar Action aid mai yaki da talauci a Najeriya ya ce, bai yi mamakin matsayin da Najeriyar ta samu kanta ba.

Najeriya dai ta yi fama da wasu manyan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya jefa kasar cikin kace-nace mai zafi a wannan shekarar.

Ciki sun hada da badakalar zargin cin hanci da rashawa game da tallafin man fetur da ya kunshi dalar Amurka miliyan dubu shida.

Sai kuma na zargin sama da fadi da kudaden fansho na 'yan sanda da ya kunshi naira miliyan dubu 24.

Zarge-zargen da kawo yanzu ba kaiga warware su ba a kotunan kasar.