Yarjejeniyar kare hakkin 'yan gudun hijira za ta fara aiki yau

'Yan gudun hijira a kasar Mali
Image caption 'Yan gudun hijira a kasar Mali

A yau wata gagarumar yarjejeniyar kare hakkin mutanen da rikici ko wata masifa ta raba su da gidajensu a kasashen Afirka za ta fara aiki.

Shekaru uku da suka gabata ne kungiyar kasashen Afirka ta amince da yarjejeniyar ta Kampala, kuma kasashen kungiyar goma sha biyar da suka hada da Najeriya da Saliyo suka sanya hannun amincewa da ita.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa dukkannin kasashen dole ne su yi dokoki, ko su gyara dokokin da suke da su ta yadda za su tabbatar da kulawa da ta dace ga mutanen da wani rikici ko bala'i ya sa suka kaura daga inda suke.

Ko da yake dai akwai doka ko yarjejeniyar kula da 'yan gudun hijira a duniya tun sama da shekaru sittin, amma wannan dokar da aka yiwa lakabi da yarjejeniya Kampala ita ce doka ta farko ta kasa da kasa da ta wajaba kan wasu kasashe su kare mutanen da suka tsere daga gidajen nasu don neman mafaka a cikin kasarsu.

Kimanin mutane miliyan goma ne aka kiyasta na gudun hijira a cikin kasashen Africa.