Fada ya sake rincabewa a kasar Masar

Riciki a kasar Masar
Image caption Magoya bayan shugaba Morsi na arangama da masu adawa a kofar fadar gwamnatin kasar Masar

Wani kazamin fada ya kara rincabewa a cikin dare a Alkahira babban birnin kasar Masar, tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Mohammed Morsi.

Mahukuntan kasar sun ce mutane hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da da kimanin dari hudu suka jikkata sakamakon fadan.

Rikicin dai ya kara bazuwa wasu sassan kasar ta Masar, inda aka kai wasu hare-hare a ofisoshin 'yayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ''Muslim Brotherhood'' dake biranen Ismailia da Suez.

Dukkannin bangarorin biyu sun yi amfani da duwatsu da ababan fashewar da aka hada da man petur wajen kaiwa juna hari.

Hakan ya biyo bayan da magoya bayan shugaba Morsi suka yi kokarin tarwatsa gungun 'yan adawa masu zanga-zanga a wajen fadar gwamnatin kasar.

Matsayin 'yan adawa

Jagoran gamayyar masu adawar na Jam'iyar National Salvation Front, Mohammed El Baradei ya ce sun dora alhakin wannan rikici ne kan shugaban kasar da gwamnatinsa, inda ya ce basu dauki matakan kare rayukan jama'a ba.

Shima dai tsohon shugaban kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa kuma memba a kungiyar gamayyar 'yan adawa ta National Salvation Front, Amr Moussa ya ce 'yan adawar sun hade ne suna kuma magana da murya guda domin su nemi 'yancin da dimokradiyya a kasar.

Masu adawar dai na ci gaba da nuna kin jinin yunkurin raba kawunan 'yan kasar ta Masar, da ma tilasta amfani da abubuwan da kundin tsarin mulki bai amince ta su ba.