An jefawa 'yan sanda abin fashewa a Kano

'Yan sandan Najeriya
Image caption Tsaro a Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria ta tabbatar da cewa wasu jami'an ta sun jikkata a wani hari da aka kai musu da safiyar yau.

Rundunar ta ce ta kuma kama mutane takwas bisa zargin su da jefawa 'yan sandan wani abun fashewa, a lokacin da suke sintiri a kan titin daya kewaya birnin Kano ta ɓangaren gabas.

Mazauna yankin dai sun ce sun ji ƙara da kuma harbe harbe.

Kwanaki huɗu ke nan a jere abubuwa su na fashewa a birnin na Kano, abinda ke nan yasa wasu ke ganin cewa lamarin tsaro a jihar na kara taɓarbarewa, sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar yace sam ba haka bane.