Ruiz zai kwashe makonni 5 bai buga wasa ba

Image caption Dan wasan gaba na Fulham Bryan Ruiz

An dakatar da dan wasan gaba na Fulham Bryan Ruiz daga buga wasa har sai cikin sabuwar shekara, bayan da ya samu ci baya a jinyar rauninda ya samu a gwiwarsa.

Manajan kungiyar Martin Jol ya tabbatar da cewar Ruiz dan shekaru 27 ya sake samun rauni a cikin raunin gwiwar da ya samu lokacin da yake buga wa kasarsa Costa Rica wasa.

'' Kamar yadda ku ka sani mun yi farin cikin fada wa kowa a makon jiya cewar, Bryan Riuz zai dawo wasa ranar litinin, amma a wajen karbar horo na wannan ranar ya sake samun wani rauni kuma dole muka aike da shi zuwa Jamus''. Inji Manaja Jol.

Wasan karshe da Ruiz ya buga dai shi ne wanda Fulham ta doke Sunderland da ci 3-0 makonni uku da suka wuce kuma yanzu zai kwashe makonni hudu zuwa biya yana jinya raunin nasa.

Karin bayani