Jirgin saman soji ya yi hatsari a Afrika ta Kudu

Taswirar Kasar Afrika ta Kudu
Image caption Taswirar Kasar Afrika ta Kudu

Wani jirgin soji dake dauke da mutane 11 ya yi hatsari a gabashin Afrika ta Kudu, inda ke da tsaunuka.

Jirgin wanda ya tashi daga Pretoria zuwa Mthatha, ya bace a ranar Laraba, sai dai an dakatar da nemansa saboda rashin kyawun yanayi.

An dai gano baraguzan jirgin a Drakensberg, wajen dake da manyan duwatsu kusa da Ladysmith a lardin KwaZulu-Natal.

Jami'ai sun musanta rahotannin farko dake cewa jirgin na dauke da wasu likitocin Nelson Mandela.

Filin jirgin sama na Mthatha dake lardin gabashin Cape na da nisan kilomita 30 zuwa kauyensu Mandela Qunu, inda yake zaune tun bayan da ya yi ritaya.