Shafin musayar hotuna na Microsoft

Microsoft
Image caption Shafin na kama da dandalin musayar hotuna na Pinterest.

Harkokin sada zumunta na kara karfafa - kamfanin Microsoft ya bude shafin musayar hotuna na internet.

Shafin na kama da dandalin musayar hotuna na Pinterest.

An shafe shekara guda ana yinsa asirce - inda za a bude shi ga dalibai a watan Mayu.

A yanzu duk wanda yake da shafin Facebook ko Microsoft zai iya shiga a daidai lokacin da shafin zai fara gogayya da Pinterest da kuma sauran shafukan musayar hotuna.

Mutum-mutumin da ya kafa tarihi

Wani mutum-mutumin na kamfanin Liquid Robotics ya kafa tarihia duniya.

Mutum-mutumin ya shafe mil 10,000 daga birnin San Francisco na Amurka zuwa Australia ba tare da an tallafa masa ba.

Ya dai shafe sama da shekara guda kafin ya isa can, inda ya rinka tattara bayanai kan yanayin tekun Pacific.

Kamfanin da ya mallake shi Liquid Robotics, na da wasu mutum-mutumin guda uku a teku, duk da cewa daya daga cikinsu ya koma Hawaii saboda matsalar da ya samu.

Karin bayani