Obama ya nuna damuwa kan rikicin Masar

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi
Image caption Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi

Shugaban Amurka Barack Obama ya nuna damuwa game da mutuwa da jikkatar masu zanga-zanga a rikicin da ya rincabe a Alkahira babban birnin kasar.

Rikicin ya kara ta'azzara cikin dare, inda masu zanga-zangar suka bankawa ofisoshin 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi wato ''Muslim Brotherhood'' ta shugaba Morsin wuta.

'Yansanda sun rika harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar da suka mamaye kofar gidan shugaban kasar da ke garinsa na haihuwa Zagazig mai kimainin kilomita tamanin daga arewacin birnin na Alkahira.

Ya gayyaci 'yan adawa

Shugaba Morsi ya gayyaci duka manyan kusoshi da shugabannin jam'iyu, matasa masu neman sauyi, da kuma manyan alkalai domin ganawa a ranar Asabar mai 8 ga watan Disamba a fadar shugaban kasa.

Ya kira taron ne domin cimma yarjejeniyar da zata hada kan kasar, wacce kuma za ta kawo karshen duk wata damuwa da rarrabuwar kawunan da aka samu.

Shugaba Morsi wanda dai ya gamu da kakkausar suka bayan wani yunkurin baya-bayan nan na karawa kan sa karfin iko a bisa doka, ya ce akawai bukatar zaman sasantawa domin shawo kan wannan rikici.

Shugaba Amurka Obama yayi na'am da kiran zaman sasantawa da 'yan adawar kasar, amma kuma ya jaddada cewa tattaunawar ta kasance wacce bata da wasu sharudda.