Hamas ta yi bikin cika shekaru 25

Image caption Taron magoya bayan Hamas

Dubban jama'a dake daga tutar Palasdinawa ne suke halartar wani babban gangami a yankin Gaza inda ake bukukuwan cika shekaru ashirin da biyar da kafa kungiyar Hamas.

Jagoran kungiyar ta Hamas, Khaled Misha'al ya samu jinjinawa sosai yayin da yake daga hannu ga dubban jama'a da suka taru.

Jagoran na kungiyar Hamas, Khaled Misha'al ya isa yankin na Gaza ne ranar Juma'a, karon farko tun bayan da yayi gudun hijira kusan shekaru arba'in da suka gaba.

Wakilin BBC yace, kungiyar Hamas tana so ne ta yi amfani da wannan gangami wajen nuna cewa, ta kafu sosai, kuma dole a yi da ita.