Ghana: 'Yan adawa sun yi gangami

A Ghana 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye ga magoya bayan babbar jam'iyyar adawa da suka yi dafifi a hedikwatar hukumar zaben kasar dake birnin Accra.

Yayin da aka kusan kidaya dukkan kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Ghana, shugaba mai ci, John Dramani Mahama yana kan gaba da tazara ba mai yawa.

Dan takarar jam'iyyar adawa ta NPP, Nana Akufo-Addo ne ke biye da shugaban kasar a yawan kuri'u.

Sai dai da aka kara kwana guda a wasu sassan kasar da aka samu tsaiko saboda tangardar na'ura.

An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a akasarin sassan kasar.

Sai dai an dan samu hatsaniya a Accra babban birnin kasar, inda 'yansanda suka yi ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya bayan 'yan adawa da suka mamaye kamfanin da ya samar da na'urorin zamanin da aka yi amfani da su a zaben.

Shugaba mai ci John Dramani Mahama, wanda ya maye gurbin marigayi John Atta Mills bayan rasuwarsa a cikin watan Yuli ne yake fafatawa da jagoran 'yan adawa Nana Akufo-Addo.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta yi hasashen cewa za a yi kan-kan-kan, kamar yadda aka yi a zaben da aka gudanar a baya, lokacin da marigayi Mr Atta Mills ya samu rinjaye kan Mr Akufo-Addo da kasa da kashi daya bisa dari.