Za a yi wata sabuwar zanga-zanga a Masar

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi
Image caption Za a gudanar da kuri'ar raba-gardama a ranar 15 ga watan Disamba

Shawarar da shugaban kasar Masar ya yanke ta soke karin ikon da ya baiwa kansa ta kasa kwantar da hankalin masu adawa da shi.

Gamayyar jam'iyyun adawar kasar ta yi kiran da a sake gudanar da wata zanga-zanga ranar Talata mai zuwa don tursasawa Shugaba Morsi ya janye shirin sa na gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Wani mai magana da yawun gamayyar ta National Salvation Front, Hussein Abdel Ghani ya sanar da matakin jam'iyyun adawar a wajen wani taron manema labarai.

Sai dai gamayyar jam'iyyu masu kishin Islama sun kira ta su zanga-zangar domin nuna goyon baya ga shugaba Morsi da kuma matakan da ya ke dauka.

Masu aiko da rahotanni sun ce babu shakka hakan zai sanya jami'an tsaron kasar cikin tsaka mai wuya.

Irin wannan zana-zanga a mokon da ya gabata ta haifar da taho-mugama tsakanin bangarorin biyu, inda aka samu asarar rayuka.