Ghana ta samu sabon Shugaban kasa

Shugaban kasar Ghana Dramani Mohama
Image caption Jam'iyyun adawa sun yi Allah wadai da sakamakon zaben

Hukumar zabe ta kasar Ghana ta bayyana cewa shugaba mai ci John Mahama ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a zagayen farko, amma babbar jam'iyyar adawa ta kalubalanci sakamakon.

Hukumar tace Mr Mahama ya lashe kashi hamsin da digo bakwai cikin dari na kuri'un da ka kada, yayinda Nana Akufo-Addo ya samu kashi arba'in da bakwai da digo bakwai, al'amarin da ya sa ba sai an je zagaye na biyu ba.

Hotunan talabijin daga kasar ta Ghana sun nuna magoya bayan Mr Mahama suna ta murna. Sai dai kuma jam'iyyar NPP ta Mr Akufo-Addo ta yi zargin an yi magudi a zaben don haka ta kauracewa bayyana sakamakon.