Nelson Mandela, ya yi kwana na biyu a asibiti

nelson mandela
Image caption nelson mandela

Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Nelson Mandela, ya yi kwana na biyu a wani asibiti da ke Pretoria bayan kwantar da shi da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

Jami'ai sun ce ana gudanar da gwaje-gwaje a kan Mista Mandela ne don gano abin da ke damun sa,sai dai kuma har ya zuwa yanzu ba a kai ga gano abin da ke damunsa ba.

Shugaba Jacob Zuma, wanda ya kai ziyara asibitin don duba Mr Mandela ya ce ya fara samun sauki.

Yanzu haka dai shekarun tsohon shugaban kasar ta Afrika ta Kudu kimanin Casa'in da hudu a duniya.