An ba dakarun Masar ikon kama mutane

sojojin Masar
Image caption Kawo yanzu dai sojin ba su sanya hannu a rikicin ba

Shugaba Muhammad Morsi na Masar ya bai wa soji ikon tsare mutane gabanin kuri'ar raba gardama da za a yi a kasar a ranar Asabar a kan daftarin tsarin mulki da ake ta takaddama a kai.

An yi sanarwa ne kwana daya kafin zanga-zangar da duka magoya bayan Shugaba Morsin da kuma 'yan hamayya suka shirya.

Tuni dai aka ga soji da tankokin da ke cikin shirin kare fadar Shugaban kasar.

Ganin babu wata alama ta kawo karshen zanga-zangar da tada zaune tsaye a kasar Masar, shugaba Morsi ya yi kira da sojojin kasar su taimaka wajen kare ma'aikatun gwamnati.

An dai sanar da sanar da sabuwar dokar da ta baiwa sojoji iko a hukumance, kuma ta kunshi ikon kama fararen hula tare da mika su ga masu gabatar da kara a kasar.

Tuni dai sojoji suka zagaye fadar shugaban kasar da tankokin yaki da kuma shingayen da suka kakkafa .

Sabon yunkurin zai kara fargaba tsakanin mutanen kasar na cewa a hankali mulkin kasar na komawa gidan jiya, shekara daya da rabi bayan hambarar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.

Duk da cewa shugaba Morsi ya soke dokar da ta kara masa karfin iko, wasu masu zanga zangar na cewa sai yayi murabus daga mukaminsa na shugaban kasa.

Karin bayani