An yi garkuwa da mahaifiyar Ngozi Okonja-Iweala

Ministar kudin Nijeriya Ngozi Okonjo Iweala
Image caption Ministar kudin Nijeriya Ngozi Okonjo Iweala

Hukumomin a Najeriya sun ce an yi garkuwa da mahaifiyar ministar Kudi ta kasar, Ngozi Okonja-Iweala, wato Farfesa Kamene Okonjo mai shekaru 82 da haihuwa.

An yi awangaba ne da Farfesa Kamene Okonjo a gidanta da ke jihar Delta a Kudu maso Kudancin kasar.

Mai magana da yawun ministar ya ce an yiwa Ngozi Okonja-Iweala barazana a baya-bayan nan, amma bashi da tabbas ko wannan na da alaka da barazanar da aka yi mata.

Najeriya na sahun gaba-gaba a duniya wurin sace mutane domin neman kudin fansa.

Wannan mummunar sana'a dai na samar da makudan kudade ga masu yinta.

Wadannan miyagun laifuka dai sun fi faruwa ne a Kudancin kasar, sai dai lamarin kan ritsa da mutane da yawa a sassan kasar da dama.

Karin bayani