Shafukan sada zumunta na amfanar 'yan sanda

Shafukan sada zumunta na amfanar 'yan sanda
Image caption Ana samun damuwa tsakanin 'yan sanda da jama'ar gari

Jami'an 'yan sanda da ke amfani da shafukan sada zumunta sosai, sun fi samun kyakkyawar dangantaka da jama'ar gari, a cewar wani rahoton bincike.

Binciken na su ya shafi kasashen Turai da dama.

Sun gano cewa a kasashen da 'yan sanda basa amfani da shafukan sada zumunta sosai, "shafukan da bana hukuma ba" sun fi farin jini.

Wani shafin Facebook da ke dauke da labarai game da 'yan sanda a birnin Berlin na kasar Jamus yana da magoya baya 15,000, a cewar rahoton.

'Wasu za su maye gurbinsu'

Binciken na cikin wani bangare na aikin da wasu da ake kira Composite (Comparative Police Studies In The EU) suka yi.

Sun tattauna da kwararrun 'yan sanda a fannin sadarwa na zamani a kasashe 13 na nahiyar Turai da suka hada da Burtaniya, da Belgium, da Jamus, da Netherlands da kuma Spain.

"Ana tattauna ayyukan 'yan sanda a shafukan sada zumunta", kamar yadda jagoran binciken Dr Sebastian Denef ya bayyana.

"Abin tambaya anan ba shi ne ko ya kamata a rinka tattauna al'amuran 'yan sanda a shafukan sada zumunta ba, sai dai yadda 'yan sanda za su shiga su amfana da wannan dama. Idan 'yan sanda basu shiga an dama da su ba, to wasu za su maye gurbinsu."

Rahoton ya ce ya kamata 'yan sanda su rinka tattaunawa da mutane a shafukan sada zumunta, ba wai kawai domin bincike ba.