Mata na cikin wani hali a Afghanistan

Wani sabon rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ya ce tsarin shari'a na cigaba da nuna gazawa wajen kare hakkokin mata a Afghanistan

Majalisar dinkin duniyar tace duk da kirkiro da wata doka shekaru uku da suka gabata data baiwa mata kariya, har yanzu wadanda suke cin zarafin matan na cin karensu ba babbaka

Duka da kuma yanka na cikin jerin laifukan da aka- fi yawan samu akan matan, sai dai rahotan ya kuma nuna cewa ana samun karuwar kashe kashen kare mutunci

A wata hira da BBC, wani mai magana da yawun gwamnatin kasar yace ya amince akwai jan aiki a gaba wajen inganta rayuwar matan kasar, amma ya hakikance cewa, an samu gagarumin ci gaba a shekaru goman da suka gabata

Karin bayani