Sojin Najeria sun maida martani

Wasu sojojin Najeriya na sintiri
Image caption Wasu sojojin Najeriya na sintiri

Hukumomin soji a Najeriya sun yi bayani a bisa zargin halaka wani direban tankar mai da wani soja ya yi a kaduna, abinda ya haifar da yajin aikin direbobin tankokin mai a jahar.

A wata takardar sanarwa da sojin suka rabawa manema labarai a Kaduna, runduna ta ɗaya ta sojojin ƙasar ta ce ta na sane da batun halaka direban na tankar mai, kuma a yanzu ta na gudanar da bincike don gano abinda ya wakana.

A yanzu dai jama'a a jahar ta Kaduna na fargabar ƙaruwar ƙarancin man da aka daɗe ana fama da shi a sanadiyyar yajin aikin da direbobin tankokin man suka shiga bayan halaka daya daga cikin 'yan kungiyar ta su.nigeria

Karin bayani