Yawan 'yan gudun hijirar Syria ya karu matuka

Wasu yara 'yan Syria masu gudun hijira
Image caption Wasu yara 'yan Syria masu gudun hijira

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya ta ce Siriyawa fiye da rabin miliyan ne suka tsere zuwa wasu ƙasashe, domin gujewa rikicin dake tsakanin gwamnati da kuma 'yan tawaye.

Shugabar Hukumar Melissa Fleming, ta ce 'yan gudun hijira Siriyawa fiye da rabin miliyan ne yanzu haka aka yi wa rajista, ko kuma suke jiran a yi masu rajista, a ƙasashe hudu dake makwaɓtaka da Syriar da kuma arewacin Afirka.

Majalisar ɗinkin duniyar ta yi gargadin cewar 'yan gudun hijirar da dama yara ne sosai, ko kuma tsofaffi tukuf, kuma ba sa iya jurewa yanayin sanyin hunturun da ake ciki.

Ta bayyana yadda wasu ƙarin mutane dubu ɗaya suka isa Jordan, cikinsu ta ce har da jarirai ashirin da biyu.

Majalisar ɗinki duniyar dai ta ce wasu ƙarin Siriyawan da dama sun tsere zuwa ƙasashen Turkiyya da Labanon da Iraqi da kuma Jordan.

Karin bayani