'Yan adawar Masar za su shiga kuri'ar raba gardama

adawa
Image caption Wasu mutane na adawa da yinkurin shugaba Morsi

Kawancen kungiyoyin 'yan adawa na Kasar Masar sun janye maganar kauracewa zaben raba gardamar da aka shirya yi kan sabon daftarin kundin tsarin mulki mai cike da kace nace, amma karkashin sharuddan da za su yi matukar wahalar cikawa.

Kawancen kungiyoyin dai na bukatar masu sa idanu na Kasashen duniya da su sa ido a zaben, wanda za a soma a ranar asabar.

Masu Jagorantar kawancen na kira ga magoya bayansu da su kada kuri'ar kin amincewa da tsarin mulkin.

Tuni dai Magidanta a Kasashen ketare suka soma kada kuri'unsu.

Wakilin BBC yace sai dai kungiyar 'yan Uwa musulmi da sauran kungiyoyin Musulumi dake goyon bayan Shugaban Kasar sun shirya tsaf, kuma ga alamu za su fita kwansu- da- kwarkwatansu, wajen kada kuri'ar amincewa da daftarin tsarin mulkin.

Karin bayani