Tashin bam a ma'aikatar cikin gida ta Syria

An ba da rahoton aukuwar jerin fashe-fashe wasu abubuwa a ma'aikatar cikin gida ta Syria, a Dimashka, babban birnin kasar.

Gidan talabijin na kasar ya ce fashe-fashe ukku aka samu kusa da ma'aikatar, daya daga cikinsu sanadin bom ne a mota.

Ma'iakatar tana a wani yanki ne a birnin Damnascus, inda aka gwabza mummunan fada tsakanin 'yan tawaye da masu goyan bayan Shugaba Bashar Al Asad.

A waje daya kuma taron kasashe fiye da dari a kasar Morocco ya amince cewa Hadakar Kungiyoyin Kishin Kasa na Syria ce kawai aka amince da ita a matsayin wakiliyar jama'ar mutanen Syriar.

Taron ya kunshi kasashen duniya fiye da dari da aka gudanar a Moroco, ya yadda zai amince da gamayyar 'yan adawar Kasar Syria, a matsayin kungiyar dake wakiltar al'ummar Syria

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce amincewa da wannan gamayya, zai bude kofar hanyar kai ayyukan agaji mafi girma, da kuma tallafin soji ga rundunar da take son ganin ta hanbarar da Shugaba Bashar Al Asad

Yace taron abokanan Syrian wanda ya kunshi kasashen yamma dana larabawa, ya samu gagarumar nasara.