CBN da NNPC sun bayyana a Majalisa

A Najeriya, wasu manyan jami'an hukumomi goma sha biyar ciki har da babban bankin kasar da Kamfanin man fetur da kuma hukumar da ke kula tasoshin ruwan kasar sun bayyana gaban kwamitin kudi na majalisar wakilai bayan an ba da warantin kama su.

Kwamitin dai ya yi zargin cewa hukumomin ba sa shigar da kudaden-shigar da suke tarawa da ya kai sama da naira tiriliyon daya a cikin baitul-malin gwamnati.

Tun da farko dai majalisar ta nemi shugabannin kamfanonin da su zo su yi mata bayani game da yadda akai da wadannan kudade amma hakan bai samu ba.

Kan haka ne yasa a wannan makon majalisar ta yi barazanar sawa a kamasu muddin su ka ki bayyana a yau din.

Yanzu haka dai kwamitin kudi na majalisar dattawan ya ce sun mika masa dukkan takaddun bayanan da suke nema wanda suka ce zuwa nan da makonm gobe za su mika rahotansu ga zauran majalisar.