Motlanthe zai kalubalanci Zuma

Image caption Kgalema Motlanthe

A Afrika ta Kudu, mataimakin shugaban kasa Kgalema Motlanthe zai kalubalanci Shugaba Zuma , wajen neman jam'iyyar ANC ta tsayar da shi dan takarar shugaban kasarta.

Mista Mothlanthe ya amince da mika sunansa da aka yi domin neman mukamin, gabanin babban taron da jam'iyyar ta ANC mai mulki zata gudanar a kusa da birnin Bloomfontein.

Duk da cewa shugaba Jacob Zuma ya na da gagarumin goyon baya a cikin jam'iyyar domin yin tazarce, kalubalantarsa da mataimakinsa Kgalema Motalanthe yake yi ya haifar da farin ciki a zukatan da dama daga cikin magoya bayan jam'iyyar ta ANC.

Fiye da jami'ai dubu hudu ne za su zabi sabon shugaba a taron jam'iyyar a mako mai zuwa.

Ana kuma sa ran sabon shugaban jam'iyyar shi ne zai jagoranci al'umar kasar a shekaru masu zuwa saboda jam'iyyar ANC ce ta yi kaka gida a siyasar kasar.

Motlantha tsohon dan kungiyar kwadago ta kasar ne wanda ya taba rike shugabancin kasar na rikon kwarya a shekarar 2008.

Ana kuma yi masa kallon dan boko mai makon dan siyasa, sai dai ya na da goyan bayan matasan jam'iyyar ta ANC.

Duk da shugaba Jacob Zuma shi ake tunanin zai lashe zaben, wasu su na ganin kalubalantarsa da Mr Motlanthe ya yi ya na nuna adawa ne da yanayin yadda shugaba Zuma ke tafiyar da mulkinsa.