An tarwatsa ma'aikata masu zanga zanga a Jos

Protests

Jami'an tsaro a Jos, babban birnin Jihar Filato sun tarwatsa dimbin ma'aikata masu zanga zanga da suka nemi hana Gwamna Jonah Jang shiga majalisar domin gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa.

Gwamnan dai ya samu shiga majalisar ne bayan da jami'an tsaron su ka jefa musu hayaki masu sa hawaye.

A cewar ma'akatan dai babu hujjar gabatar da kasafin kudin domin gwamnatin ta kasa biyansu kudadensu na albashi na watanni bakawan da suka kwashe suna yajin aiki na neman karin albashi, mafi karanci na Naira dubu sha takwas.

Mutane da dama ne suka jikkata a lokacin hargitsin, wasu rahotanni kuma na cewa an lakada ma kwamishinan ayyyukan gona na jihar ta Pilato duka, lokacin da yake ratsawa ta cikin masu zanga zangar.

Wannan na zuwa ne yayin da uwar kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC ta fitar da wata sanarwa mai dauke da zafafan kalamai na cewa gwamnan na jihar Filato hatsari ne ga dimokuradiyyar Nijeriya.

Ranar Talata ne sauran kungiyoyin kwadago suka bi sahun kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE wajen yajin aikin a jihar ta Flato.