Syria na harba makamai masu linzami

Malamai masu linzami a Syria
Image caption Malamai masu linzami a Syria

Jami'an Amurka da na kungiyar tsaro ta Nato sun ce dakarun gwamnatin Syria na amfani da makamai masu linzami masu cin gajeren zango a fadan da suke yi da 'yan tawaye.

Jami'an, wadanda suka yi magana bisa sharadin ba za a bayyana sunayensu ba, sun ce an harba makami mai linzami samfurin Scud ne daga kewayen birnin Damascus zuwa yankunan da ke hannun 'yan tawaye a arewacin kasar.

Ba tare da ta ambaci makamai masu linzami ba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland.

Yayinda gwamnatin Syria ke kara shiga halin takura, muna ganin yadda take kara amfani da munanan makamai.

Karin bayani