Za a fara wallafa jaridar China a Afirka

Taron kasar China kan Afirka
Image caption Taron kasar China kan Afirka

Babbar jaridar da ake wallafawa da turanci a kasar China, China Daily, za ta fara buga labarai na musamman kan Afirka na mako-mako, a birnin Nairobi na kasar Kenya.

A 'yan shekarun nan dai China ta kara yawan harkokin yada labaranta a Afirka, saboda muhimmancin nahiyar wajen kasuwanci da samar da albarkatun kasa.

Ita dai jaridar wacce za a rika bugawa mako-mako za kuma a iya karanta ta ta hanyar intanet, inda za a raba ta zuwa kowacce kusurwar Afirka.

China Daily ta ce daya daga cikin manufofin kafa jaridar shi ne yin bayani game da dangantaka ta kut-da-kut da ke tsakanin China da Afirka, wacce a cewarta, na da sarkakiya, kana ba safai ake fahimtarta ba.

Wannan dai shi ne shiri na baya-baya cikin shirye-shirye game da watsa labarai da China ta bullo da su akan Afirka.

A farkon shekarar da muke ciki, gidan talabijin din China Central Television ya kaddamar da wata tashar talabijin mai suna CCTV Africa.

Tashar wacce ke da hedkwata a Kenya, ta dauki 'yan Afrika da dama aiki, kuma masu gabatar da shirye-shiryenta na gabatarwa ne da harshen turanci.

Manufar Gidan Talabijin din kasar China

Manufar gidan talabijin din a cewar mahukuntansa, ita ce ya gabatar da tsagwaron labaran kasar China ga Africa, kana ya kuma gabatar da tsagwaron Africa ga duniya.

Shi ma kamfanin dillancin labaran China, Xinhua, yana fadada harkokinsa a Africa, haka ma gidan radiyon China.

Kazalika China ta kaddamar da wasu sabbin shirye-shirye kan yadda za a ingata harkar yada labarai, cikinsu har da sanya manya-manyan talabijin a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labaran China Xinhua ya kulla kawance da kamfanin wayar salula na Kenya mai suna Safaricom, don samar da labarai ga masu amfani da wayoyin salular.

China ta kuma sanya hannu a harkokin watsa labarai na Afrika ta wadansu hanyoyin na daban.

Dubban 'yan jarida daga Afrika ne suka samu tallafin karo karatu a China.

Haka kuma ta kashe miliyoyin kudi akan harkokin watsa labarai da sadarwa a Afirka, tun daga Habasha zuwa Ghana, daga Kenya zuwa Zambia.

Wasu kasashen kamar Habasha na da tsauraran dokoki kan watsa labarai, yayin da wasu kuma irin su Ghana ke da sassauci ga kafafen watsa labarai.