An kashe dan majalisa a Kano

Taswirar Kano
Image caption A watan Nuwamba an kashe dan majalisar jihar mai Garko

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga sun harbe har lahira waklin karamar hukumar Gaya a majalisar dokokin jihar Alhaji Dan Ladi Isa Kademi.

Wakilin BBC a Kano yace 'yan bindigar sun harbe dan majalisar ne da yammacin ranar Juma'a.

Rundunar yan sandan jihar ta ce wasu mutane ne a babur suka same shi a kofar gidan sa na hutawa a Hotoro da ke birnin na Kano, inda suka bude masa wuta sannan suka tsere.

Kafin zabensa a matsayin dan majalisa, Dan Ladi Kademi, ya zama shugaban karamar hukumar Gaya kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na Kano.

A watan Nuwamba ma dai wasu 'yan bindiga sun kashe dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar karamar Hukumar Garko.

Babu wata kungiya da ta dauki nauyin harin, amma jihar ta Kano ta sha fama da hare-hare masu nasaba da kungiyar Boko Haram.

Kungiyar dai na kai hare-hare ne kan jami'an tsaro, sai dai fararen hula da dama sun mutu a sakamakon ayyukan kungiyar.

Karin bayani