An gudanar da gangami a Koriya ta Arewa

Kaddamar da Tauraron dan adam a Korea ta Arewa
Image caption Kaddamar da Tauraron dan adam a Korea ta Arewa

An gudanar da wani gagarumin gangami a Pyonyang, babban birnin kasar Korea ta Arewa, domin bikin murnar kaddamar da tauraron dan adam na farko a farkon wannan makon.

Gidan Talabijin na kasar ya nuna dubun dubatar mutane sun taru a dandalin Kim il Sung suna sauraron jawabai masu dauke da jinjina ga nasarar da kasar ta samu.

Dubun dubatar jama'ar ne suka yi layi a fadin dandalin na Kim il Sung, suna tsaye cik a cikin sanyi, yayinda jami'an ke gabatar da jawabai masu dauke sakon taya murna da fatan alheri ga kasar game da nasarar da ta samu na kadamar da tauraron dan adam.

Wannan wasu alamu ne na ci gaba a fannin kimiyya ga kasar Koriya ta Arewar, kana duka suna nuna godiyarsu kan abinda suka ce na namijin kokarin shugabanninsu.

Jama'ar dai na makale da. jajayen tutoci a kansu, dauke da kwalayen da aka rubuta take daban-daban dake nuna farin cikinsu, sai dai da alamu fuskokinsu basa cike da walwala.

A ranar Laraba ne dai aka kaddamar da tauraron dan adam din a birin Pyonyang, wanda kuma ya haifar da matukar suka daga kasashen Amurka da Koriya ta Kudu.

Kasashen dai sun ce sun yi amannar cewa hakan wata hanya ce ta yin rufa-rufa game da kokarin da Koriya ta Arewan ke yi domin yin gwajin makamai masu linzami.

Kawayen kasar Koriya ta Arewan ma dai sun nuna matukar damuwarsu.

Ana sa ran Kwammitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai dauki wasu matakai kan martanin da suka biyo bayan wannan mataki da kasar ta Koriya ta Arewa ta dauka na kaddamar da tauraron dan adam din.

Sent from my BlackBerry wireless device from MTN