Ana zaben raba gardama a Masar

Rahotanni na nuna cewa dimbin jama'a ne suka fita domin yin zaben rabagardama kan sabon kundin tsarin mulki a Masar, batun da ya janyo rarrabuwar kawuna a kasar da ma tashin a hankali a sakamakon zanga zanga.

A yanzu an tsawaita lokacin kada kuri'ar da sa'o'i biyu a biranen Alkahira da Iskandariyya, da ma sauran larduna takwas inda Misirawan ke zabe.

An tsaurara matakan tsaro, amma komai na tafiya ba tare da wata hatsaniya ba.

Shugaba Morsi da jam'iyyaras ta Yan Uwa Musulmi na goyon bayan kundin tsarin mulkin, yayinda 'yan adawa ke cewa kundi ne da masu ra'ayin Islama suka tsara cikin gaggawa, ba tare da yin wani tanadi na bada isasshiyar kariya da 'yancin Bil'adama ba.