Dan bindiga ya hallaka yara ashirin a Amurka

Daya daga cikin daliban makarantar Sandy Hook da suka tsira
Image caption Daya daga cikin daliban makarantar Sandy Hook da suka tsira

Wani dan bindiga ya hallaka kananan yara kimanin ashirin da kuma manya shidda a wata makarantar firamare dake jihar Connecticut, arewa maso gabashin Amurka.

Lamarin ya abku ne a makarantar firamare ta Sandy Hook dake garin Newton, wanda dalibanta masu shekaru kimanin biyar zuwa goma ne.

'Yansanda sun ce dan bindigar wanda mai kimanin shekaru ashirin ne, ya bindige kansa bayan ya aikata ta'asar, yayinda aka gano wata gawa dake da alaka da shi a wurin.

Wannan ya kasance kisa mafi muni na baya-baya a tarihin Amurkar.

Shaidu sun ce sun ji karan harbe-harbe kamar sau dari, kana sun ga yara 'yan makaranta cikin kaduwa na ta gudun ransu daga Makarantar.

Kafin kai wannan hari dai an bayyana cewa dan bindigar ya hallaka mahaifiyarsa, wacce ke koyarwa a wannan makarantar.