Jam'iyyar Shinzo Abe ta yi nasara a Japan

Shinzo Abe
Image caption Shugaban jam'iyyar LDP a Japan

Jim kadan bayan bayyana gagarumar nasarar da jam'iyyar LDP ta samu a zaben kasar Japan, jagoranta, wanda ake kyautata zaton shi zai zamo praministan kasar na gaba, Shinzo Abe , ba tare da bata lokaci ba, ya furta cewa Japan ce ta mallaki wasu tsibirai da suke takaddama da China game da su.

Wannan nasarar da jam'iyyar LDP ta yi dai zata ba Shinzo Abe wata sabuwar damar aiwatar da manufofinsa na kishin kasa.

Mr Abe ya ce zai mai da hankali wajan sake gina tattalin arzukin kasar da ya tsaya cik.

Lokacin wata hira ta talabijin Mr Abe yayi kira ga gwamnatin China da ta kara kokari wajen kyautata dangantakarta da Japan, amma ya ce ba niyyar jam'iyarsa ce ta ga ta kara dagula al'amurra ba.

A wani sharhi, kampanin dillancin labarun China, Xinhua ya ce samun gwamnati da ba ta damu da zaman lafiya ba a Japan, zai iya yin illa ga yankin.

Karin bayani