Bincike kan mutuwar gwamnan Kaduna Patrick Yakowa

Marigayi gwaman jihar Kaduna Patrick Yakowa
Image caption Marigayi gwaman jihar Kaduna Patrick Yakowa

Shugaba Goodluck Jonathan ya bada umurnin gudanar da bincike kan hadarin jirgin saman sojin ruwan Najeriya da ya hallaka gwamnan jihar Kaduna Mr Patrick Yakowa da tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Janar Andrew Azazi.

Umarnin na kunshe ne a sanarwar ta'aziyyar da ta fito daga fadar shugaban Najeriyar.

Cikin wadanda suka hallaka tare da gwamna Yakowan da tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaron Najeriyar, Janar Anrew Owoye Azazi a hadarin jirgin sun hada da dogarawansu, Dauda Tsoho da Warrant officer Mohammed Kamal, da kuma matukan jirgin, Kwamanda Murtala Mohammed Daba da Laftanal Adeyemi Sowole.

Marigayi Patrick Yakowa, shine gwamna na farko zababbe daga kudancin jahar ta Kaduna.

Nan gaba kadan ne dai za a rantsar da mataimakinsa Alhaji Mukhtar Lamaran Yero, a matsayin sabon gwamnan jihar ta Kaduna.

Hadarin jirgin dai ya abku ne da yammacin Asabar a jihar Bayelsa mai arzikin man petur dake kudancin Najeriyar.