Bom ya hallaka mata tara a Afghanistan

Harin bom a Afghanistan
Image caption Harin bom a Afghanistan ya hallaka mata

Jami'ai a Afghanistan sun ce yara mata tara sun mutu kuma wasu guda uku sun samu raunuku bayan wani tashin bam da aka dasa gabashin ƙasar ya tashi.

Wani mai magana da yawun gwamnan yankin Nangarhar ya ce yaran waɗanda suke tsakanin shekaru tara zuwa goma sha ɗaya na ɗiban itacen girki ne a lokacin da wani bam da aka dasa a ƙasa ya tashi.

Ba'a dai tantance ko bam ɗin na daga cikin waɗanda aka dasa a zamanin Soviet ba, ko kuma ƙungiyar Taliban ce ta dasa a kwanannan.

Karin bayani