Minista ta yi ƙarin haske kan sace mahaifiyar ta

Image caption Ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala

Ministar harkokin kuɗin Najeriya dai ta ce mutanen da su ka yi garkuwa da mahaifiyarta a makon jiya, sun kwashe tsawon lokaci su na musguna mata, kana su ka shaida mata cewa dole ne sai Ministar ta bayyana a kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin, sannan ta ayyana cewa ta sauka daga muƙaminta kafin su saki mahaifiyar ta ta.

Mrs. Ngozi Okonjo Iweala, wacce ta yi hira da manema labarai ɗazu a Abuja, ta ƙara da cewa, lokacin da mahaifiyarta ta tambayi mutanen dalilin da zai sa 'yar ta, ta yi murabus, sai su ka ce saboda taƙi biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ga waɗansu mutane.

An dai kama mahaifiyar ministar watau Farfesa Kamene Okonjo mai shekaru 83 a duniya ne , ranar tara ga watan da muke ciki a gidanta da ke birnin asaba na jihar Delta, kuma ta kwashe kwanaki biyar a hannun mutanen da suka yi garkuwar da ita.

An dai kama Farfesa Kamene ne a daidai lokacin da shugaban ƙasar Dr Goodluck Jonathan ya nemi majalisar dokokin ƙasar ta ƙara masa kuɗi don cike gibin da aka samu a kasafin kuɗin da aka ware don bayar da tallafin man fetur da su ka kai naira biliyan ɗari da sittin da ɗaya.

Karin bayani