Hare-hare: Obama zai yi amfani da karfin iko

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Obama ya yi alkawarin amfani da karfin ikonsa wajen hana kara abkuwar hare-haren bindiga kamar irin wanda ya faru a garin Newton dake jihar Connecticut, arewa maso-gabashin Amurka.

Wani dan bindiga ne dai ya hallaka mutane a shirin da shida a wata makarantar firamare ranar Juma'a, lamarin da ya tayar da hankulan jama'a da dama.

Yayinda yake jawabi a wani taron addu'oin sosa rai a garin Newton, Mr. Obama ya ce idan dai har ana son kawo karshen aukuwar abubuwan bakin ciki irin wannan, dole sai Amurka ta sauya dokar nan da ta shafi mallakar bindiga.

Shugaba Obaman ya ce nan da 'yan makonni, zai yi amfani da duk wani karfin ikonsa wajen saka ma'aikata, kama da jami'an tsaro, zuwa wasu kwararru kan halayyar dan adam, da masu ilmantar da iyayen yara, wajen kokarin hana sake abkuwar lamarin.