Ba dokar hana mallakar bindiga! Obama

Masu makoki a Amurka
Image caption Masu makoki a Amurka

A yau ne za'a yi jana'iza ta farko ta wasu daga cikin wadanda aka kashe a harbe haben bindiga a jahar Connecticut ta kasar Amirka.

Shugaban Amirkan Obama ya yi jawabi mai sosa zukata a wani taron adduoi wanda ya hada da mabiya addinai daban daban a garin Newton na jihar Connecticut domin neman rahama ga mutanen da suka rasu, bayan harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 yawancinsu kananan yara a wata makarantar Firamare.

Mr Obama ya shaidawa masu zaman makokin cewa babu wata doka da za ta iya kawar da ta'asa a duniya ko kuma hana aikata abin kaicho.

Sai dai yace wannan ba zai zama madogara ta kin daukar mataki ba.

Yace domin ganin an kawo karshen wannan ta'annati akwai bukatar Amirka ta sauya.

Sai dai kuma Shugaban bai ambaci matakin takaita mallakar bindiga ko kuma wata doka takamammiya ba a yayin da yake maganar amfani da dukkan karfin ikonsa a matsayin shugaban kasa.

Wata 'yar Majalisa a Oregon inda wani dan bindiga ya kashe wasu mutane biyu a makon da ya gabata tace lallai zai Amurka ta sake duba dokar Malakar makai inda tana so a kawo karshen kashe-kashen da ake yi.

Karin bayani