ICC ta wanke Ngudjolo Chui na Congo

Kotun ICC a Hegue
Image caption Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na sauraron karrakin yaki musamman daga nahiyar Afrika

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC a Hague ta wanke tsohon shugaban masu dauke da makamai na Congo, Mathieu Ngudjolo Chui.

Kotun ta wanke shi ne daga laifukan da suka shafi aikata laifukan yaki, wanda suka shafi kisan mutane 200 a kauyen Bogoro a shekarar 2003.

Kauyen dai na lardin Ituri ne, mai arzikin ma'adanai a jamhuriyyar democradiyyar Congo.

Mista Ngudjolo dai ya musanta bada umarnin kai harin, yana mai cewa sai bayan an kwashe kwanaki ma sannan ya san an kai harin.

Masu shigar da kara dai sun ce ya yi amfani da yaran dake tilastawa shiga aikin soji ne wajen aikata kisan.

Alkalin kotun, Bruno Cotte ya ce kotun ta wanke Mista Ngudjolo ne game da tuhume-tuhumen da ake masa, saboda masu shigar da kara sun kasa gamsar da kotun cewa ya na da laifi wajen kai harin.

Inda ya bada umarnin sakinsa nan take.

Rikicin na Ituri wani bangare ne na yakin da aka yi ta fama da shi a jamhuriyar Congon, bayan kisan kiyashin da aka yi a makociyar kasar, Rwanda a shekarar 1994.

Yakin ya kunshi sojoji da mayakan sa kai daga kasashe da dama dake makotaka da kasar.