An yi ma wata mata fyade cikin bus a Indiya

Masu fafutukar kare hakkin mata a Indiya.
Image caption Masu fafutukar kare hakkin mata a Indiya.

A kasar India ana ta kiraye kirayen zartar da hukuncin kisa a kan wadanda aka samu da laifin fyade bayan wani cin zarafin da aka yi wa wata matar da aka bar ta mutu kwakwai rai kwakwai.

Wasu gungun maza ne suka yi wa wadda abun ya shafa fyade yayinda take komawa gida daga sinima, tare da saurayinta.

An kama mutane hudu tare da direban motar, kuma ministan cikin gida na kasar ta Indiya Sushil Kumar Shinde ya ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu ba tare da bata lokaci ba.

Wannan batu dai ya tada hankalin jama'a a Indiya, abin da ya sa tafka wata muhawara a gaban majalisar dokokin kasar.

A can ne ma wata yar majalisar, Jaya Bachchan ta bukaci kawo karshen abin da ta kira abin kunya, ganin yadda iyaye da yayye da sauran dangi ke da hannu a irin wannan aika aika.

Rahotanni dai sun ce an yi wa sama da mata dari shidda fyade a birnin Delhi a bana.

Ana danganta lamarin da irin daukar da ake yi wa mata ba a bakin komai ba a Indiya, kuma ana cewa 'yan sanda ba sa daukar matakan da suka dace na ba su kariya.