An sace ma'aikatan Hyundai 6 a Najeriya

Image caption 'Yan takifen yakin Neja Delta mai arziki mai a Najeriya sun sha sace 'yan kasashen waje a kasar.

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun sace wasu mutane hudu 'yan kasashen waje ma'aikatan kamfanin kere-kere na Korea ta kudu mai suna Hyundai.

Haka kuma cikin wadanda aka sacen sun hada da wasu 'yan Najeriya biyu, suma dai ma'aikata ne a kamfanin.

Jami'an 'yan sanda sun ce an sace mutanen ne a jahar Bayelsa mai arzikin danyen mai dake kudancin kasar a ranar Litinin.

''Da misalin karfe uku da rabi na rana ne wasu mutane dauke da makamai suka afkawa wani sansanin kanfanin na Hyundai da cikin wani sunkurun daji daura da gabar tekun Atilantika, inda suka sace mutanen shida'' Inji mai magana da yawun 'yan sanda a jahar ta Bayelsa Fidelis Odunna.

Sai dai Mr. Odunna dai bai bayyana kasashen da 'yan kasashen wajen suka fito ba; amma galibin wadanda ba 'yan Najeriya ba da ke aiki da kanfanin na hyundai 'yan kasar koriya ta Kudu ne.

Kamfanin na Hyundai a birnin Seoul na Koriya ta kudu ya tabbatar da sace ma aikatan nasa, amma yace ga alamu an saki daya daga cikin 'yan Najeriyar biyu.

Satar mutane dai ta zama ruwan dare a kasar wadda ita ce ta daya a arzikin mai a Afrika.

Karin bayani