Gawar Patrick Yakowa ta isa Kaduna

Akwatin gawar Yakowa
Image caption Gawar Marigayi Yakowa ta iso Kaduna

Gawar marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Patrick Ibrahim Yakowa, ta iso mahaifarsa ta Kaduna daga Bayelsa, inda ya mutu a hadarin jirgin sama.

Gawar tsohon gwamnan dai ta sami rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin jahar Bayelsan.

Tun farko dai an shirya kai gawar Kadunan ne a jiya, amma aka fasa domin bayar da damar gudanar da wani taron bankwana da majalisar zartarwar jihar Bayelsan ta shirya yi masa a fadar gidan Gwamnatin jahar.

A ranar alhamis ne dai ake shirin binne gawar marigayi Patrick Ibrahim Yakowa a mahaifarsa dake Fadan Kagoma a karamar Hukumar Jema'a.

Mr Yakowa ya rasu ne tare da wasu mutanen biyar da suka hada da Tsohon Mai ba shugaban Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Janar Andrew Azazi mai ritaya.

Karin bayani