'BBC ta gaza kan batun Newsnight'

newsnight
Image caption Shirin Newsnight na kayatar da masu sauraro a Birtaniya

Wani rahoton bincike ya ce an samu "rudani da rashin tabbas" a BBC, game da yadda shirin talabijin na Newsnight ya fasa gabatar da wani shiri da ya shafi BBC.

Sakamakon binciken da kwamitoci biyu suka gudanar, sun yi matukar sukar lamirin irin kura-kuran da aka tafka game da shirin da Newsnight ya gudanar kan zargin lalata da aka yi wa wani tsohon mai gabatar da shirye-shiryen talabijin na BBC Jimmy Savile.

A sakamakon haka, BBC za ta sauya ma edita da mataimakin edita na shirin wuraren aiki.

Wannan lamari ne dai ya kai ga murabus din darakta janar na hukumar yada labaran ta BBC, George Entwistle.

Rahoton kwamitin na biyu ya ta'allaka ne a kan wani shirin da aka watsa wanda ya zargi wani tsohon dan majalisa da lallata da kananan yara, amma kwamitin ya ce shirin bai da cikkakiyar hujjar ajiye labarin sannan kuma an samu rudani tsakanin shugabannin da ke kula da shirin.

A sakamakon sukar da aka yiwa shirin ne wani mataimakin direkta a BBC ya ajiye aikinsa a yau (Laraba).