Chadi ta tura sojoji Afrika ta Tsakiya

Image caption Shugaban Jamhuriyar Chadi Idris Deby a hagu tare da takwaransa na Faransa Francois Hollande

Jamhuriyar Chadi ta aike da sojoji zuwa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ranar Talata domin taimakawa sojojin kasar tunkarar mayakan 'yan tawaye wadanda ke matsowa.

Ranar Talata wata gamayyar kungiyoyi masu dauke da makamai ta mamaye garin Bria inda ake hakar Diamond bayan ta kwace iko da wasu garuruwa a arewacin kasar a makon jiya kuma 'yan tawayen na barazanar tunbuke shugaba Faransuwa Bozize.

Kimanin motoci ashirin ne dake dauke da sojojin kasar Chadi wadanda ke tare da manyan makamai suka ketara kan iyaka zuwa cikin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, domin taimakawa tunkarar 'yan tawayen wadanda kilomita dari ukku ne kawai suka rage su kai babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce shugaba Francois Bozize ne da kansa yayi kira ga makwabciyar ta sa daga arewa da ta kawo masa dauki.

Kwace garuruwa

Bangarorin 'yan tawayen sun kwace akalla garuruwa hudu kusa da iyakar kasar da Chadi a makon jiya, kuma suka kwace iko da garin Bria mai arzikin ma'adinin diamond da kuma wani sansanin soji.

Sojojin gwamnati sun arce daga inda suka ja daga bayan musayar wuta mai zafin gaske.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Chadi ta aike da sojanta zuwa cikin yankin makwabciyar ta ta ba.

Ita ce ta taimakwa Mista Bozize ya karbi ragamar mulkin kasar shekaru tara da suka wuce,da kuma a shekara ta 2010 lokacin da ya fara fada da wadannan 'yan tawayen.