Neman gudunmawa ga 'yan gudun hijarar Syria

syria
Image caption Akwai miliyoyin 'yan gudun hijira a cikin Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani asusun tara dala biliyan daya domin taimakawa 'yan gudun hijira daga kasar Syria.

A cewar majalisar kudin zai taimakawa mutane sama da miliyan daya ne a watan shidan farko a badi wadanda suka shiga mawuyacin hali.

Dubban 'yan gudun hijira ne dai a kullum suke ketarewa zuwa kasashen dake makwabtaka da Syriar domin neman mafaka.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya mai kulla da shiyar Syria ya ce, baya ga mutanen da suka yi kaura daga kasar, akwai sama da mutane miliyan hudu da basu da matsuguni a cikin kasar ta Syria.

Karin bayani