Taliban za ta yi sulhu da Northern Alliance

Image caption Mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan

Jagororin kungiyar Taliban a Afghanistan za su hau teburin shawarwari da tsofaffin abokan gabarsu na kungiyar Northern Alliance.

Wakilan shugaban kungiyar Taliban, Mullah Omar, za su yi wata tattaunawa ta sirri ne a Paris da jagororin kungiyar ta Northern Alliance da kuma jami'an gwamnatin Afghanistan.

Kungiyar ta Northern Allinace ce dai ta taimaka wajen fatattakar gwamnatin Taliban yayin mamayar da Amurka ta jagoranta a shekarar 2001.

Ana kyautata zaton tattaunawar bangare ne na kokarin da Taliban da sauran bangarorin kasar ta Afghanistan ke yi, don shirya wa janyewar dakarun kungiyar tsaro ta NATO.

Karin bayani