Mutane 10 sun mutu a hadarin mota a Bauchi

Taswirar jihar Bauchi
Image caption Rashin kyawun ababen hawa na daga cikin abubuwan da ke haifar da hadura a Najeriya

Akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hadarin mota a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.

Wasu mutanen da dama ne kuma suka jikkata a hadarin wanda aka ce ya faru ne tsakanin wasu motoci biyu da kuma wani babur a yankin Alkaleri.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haduran hanya ta Najeriya reshen jihar Bauchi, Ibrahim Usman Gaidam, ya shaida wa BBC cewa mutane 18 ne hadarin ya ritsa da su, ciki harda mata da kananan yara.

"Dibar mutane fiye da yadda ya kamata da gudu fiye da kima, na daga cikin musabbabin hadarin," a cewar Mr Ibrahim Gaidam.

Najeriya ce kasa ta biyu a duniya da ke fama da yawan haduran mota a cewar Hukumar lafiya ta duniya.

Kuma wakilin BBC a yankin na Arewa maso Gabas, Ishaq Khalid, ya ce rashin kyawun hanyoyi da tukin ganganci, da sabawa doka, da rashin kyawun ababen hawa na daga cikin abubuwan da ke haifar da hadura a kasar.

Karin bayani