Gwamnan Babban Bankin Ecuador ya yi murabus

Raael Correa
Image caption Gwamnan babban bankin ecuador ya yi murabus

Gwamnan babban bankin Ecuador ya yi murabus, bayan ya amsa cewa ya yi karyar samun karantun digiri a fannin tattalin arzuki.

Pedro Delgado ya nemi afuwa na bada takaddun bogi lokacin da ya nemi shiga makaranta a Costa Rica, sama da shekaru 20 da su ka wuce.

Ya kammala karatun digirinsa na biyu a wajan, sai dai makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta INCAE ta gano cewa ya yi karya wajan neman shiga makarantar.

Shugaba Rafael Correa ya kwatanta wannan labarin a matsayin wani babban abin kunya ga gwamnatin juyin juya halin kasar.